Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa adadin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya ragu matuƙa sakamakon ci gaba da gudanar da gwaje-gwaje da bincike.
A cewarsa, adadin waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar ya ragu zuwa mutum 116 kacal, idan aka kwatanta da sama da mutum 1,000 da aka ruwaito a makon da ya gabata.
Ya ƙara da cewa sakamakon gwaje-gwajen da aka gudanar ya tabbatar da cewa mutum 340 ne suka kamu da cutar Ebola a ƙasar, yayin da mutum 60 suka rasa rayukansu sakamakon cutar.
Tedros ya ce ziyarar da ya kai yankunan da annobar ta fi kamari ta ba shi ƙarfin gwiwa kan irin ƙoƙarin da hukumomin lafiya da abokan hulɗarsu ke yi wajen shawo kan yaduwar cutar.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa har yanzu akwai ƙalubale da dama, musamman wajen faɗaɗa gwaje-gwaje da kuma bibiyar mutanen da suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar domin hana ci gaba da yaɗuwarta.