National Emergency Management Agency ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su fara ɗaukar matakan kariya domin kaucewa matsalar ambaliya, bayan hasashen da aka yi cewa sama da jihohi 30 na iya fuskantar mummunar ambaliya a daminar bana.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, shugabar NEMA, Zubaida Umar, ta buƙaci jihohin da su gaggauta ɗaukar matakai domin rage illar ambaliyar da ake hasashen za ta afku a wasu yankunan ƙasar.
Sanarwar ta bayyana cewa matakan da ake sa ran jihohin za su ɗauka sun haɗa da ƙarfafa tsaftar muhalli a kai a kai, gyaran magudanan ruwa da kuma buɗe hanyoyin da ruwa ke bi.
Shugabar NEMA ta kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, malaman addini, ƙungiyoyin matasa, kafafen yaɗa labarai da kamfanoni masu zaman kansu da su mara wa ƙoƙarin hukumar baya wajen wayar da kan jama’a da kare afkuwar ambaliya a Najeriya