Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa an kammala shirin nan da aka daɗe ana jira na sauya tsarin yada shirye-shiryen talabijin daga analog zuwa dijital (wato Digital Switch Over, DSO) a Nijeriya, sai ƙaddamarwa a watan gobe.

Ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar musamman a cibiyoyin aiki na NIGCOMSAT da ke Cibiyar Sararin Samaniya ta Obasanjo a Abuja ranar Laraba.

Da yake bayyana wannan cigaban a matsayin wani muhimmin sauyi a fannin watsa shirye-shirye a Nijeriya, Ministan ya bayyana lamarin da wani babban cigaba a ajandar gyaran da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi a fannin yaɗa labarai