Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta sake jaddada kudirinta na yin aiki tare da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, gabanin babban zaben shekarar 2027 domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe cikin lumana a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abimbola Adebisi, ya fitar a ranar Laraba bayan wata ziyarar ban girma da jami’an INEC suka kai hedikwatar rundunar da ke Ikeja.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Tijani Fatai, ya karbi tawagar INEC karkashin jagorancin kwamishinan zabe na jihar Legas, Abayomi Salami.