Kwamitin harkokin Noma da Albarkatun kasa na Majalisar Dokokin Jihar Kano ya nuna damuwa kan barkewar cuta mai suna Tuta Absoluta da ke lalata gonakin tumatir a jihar.
Shugaban kwamitin, Ahmed Ibrahim ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin kan barkewar cutar a gaban majalisar.