Wannan na cikin sanar da Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta fitar.

Sanarwar ta ce al’ummar Nasarawa Tudu, Nasarawa Rahi, Kofar Attahiru, Danyali, Illela Takalmawa da Mai Banche ne lamarin ya shafa, inda mutane da dama suka samu raunuka yayin da gidaje da dama suka lalace.

Hukumar ta ce ta tattauna da shugabannin al’umma da waɗanda abin ya shafa domin tantance irin tallafin gaggawa da ake buƙata musamman matsuguni, kayan amfanin gida da tallafin lafiya.