Matakin murabus da shugaban majalisar ya ɗauka, ya sharewa tsohon firaminista Ousmane Sonko hanya na neman kujerar shugabancin majalisa, inda jam'iyyarsa ta Pastef ke da gagarumin rinjaye.

Wata sanarwa da aka fitar a yammacin jiya Lahadi ta nuna cewar, an gayyaci ƴan majalisar a gobe Talata, don gudanar da wani zama na musamman da za a rantsar da Sonko a matsayin ɗan majalisar, da kuma zaɓen sabon shugaban majalisar.

Faye dai ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a shekarar 2024 tare da goyon bayan Sonko, wanda da ace ba a hana shi tsayawa takara a zaɓen ba saboda zargin laifi, da zayyi wuya ba shi zai lashe zaɓen ba.

Jam’iyyarsu ta Pastef ta yi nasara a zaɓen ne bisa alƙawarin kawo sauyi a siyasar ƙasar da yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma farfaɗo da tattalin arziƙin da ya taɓarɓare.



To sai dai a ƴan watannin nan ruwa ya yi tsami tsakanin aminan junan, lamarin da ya kaiga shugaba Bassirou Diomaye Faye ya kori Ousmane Sonko daga muƙamin Firaminista da ya naɗa shi.

Sonko dai ya zargi Faye da gazawa a salon shugabancinsa, musamman a yadda ake jan ƙafa wajen shari'un cin hanci da rashawa da ake yi wa jami'an gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Macky Sall.