Dakarun Najeriya sun kuɓutar da aƙalla mutum 92 daga hannun mayaƙan Boko Haram a wani samame da suka kai a jihar Borno, tare da kwance nakiyoyi da aka dasa a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya da ke ƙaramar hukumar Biu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce waɗanda aka ceto sun haɗa da maza 52 da mata 33 da kuma yara bakwai.

Sanarwar ta ce dakarun sun gano mayaƙan ne yayin da suke tilasta wa mutanen da suka sace tafiya zuwa cikin daji tare da wasu ababen hawa.

Rahotanni sun ce bayan da mayaƙan suka fahimci cewa sojoji na binsu, sai suka dasa nakiyoyi guda uku a hanya domin hana dakarun ci gaba da bibiyarsu, amma jami’an sojin sun yi nasarar kwance su ba tare da wata matsala ba.

Hakan ya tilasta wa mayaƙan tserewa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

A wani lamari dabam kuma, jami’an tsaro a jihar Kwara na ci gaba da neman wasu ƴan bindiga da suka kai hari wani masallaci a ƙauyen Ikiran da ke ƙaramar hukumar Ekiti, inda suka kashe mutum uku tare da sace masu ibada 15.