Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya sun kashe aƙalla mayaƙa 12 da ake zargin ƴan ta’adda ne tare da ƙwato makamai a wani samame da suka kai a jihar Borno.
An gudanar da aikin ne a yankin Kirawa da ke ƙaramar hukumar Gwoza, bayan wasu da ake zargin mayaƙan Daesh-WAP/Boko Haram ne sun yi ƙoƙarin kai hari sansanin Bataliya ta 153 da sauran jami’an tsaro da ke yankin kan iyakar Najeriya da Kamaru.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce dakarun sun gano harin cikin gaggawa tare da mayar da martani mai ƙarfi wanda ya tilasta wa maharan tserewa.
Sanarwar ta ce bayan artabun, an tabbatar da kashe mayaƙa 12 yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbi.
Ta ƙara da cewa an ƙwato bindigogin AK-47 da bindigar PKT da na’urorin harba rokoki da kuma harsasai masu yawa.
Rundunar ta ce harin ya sake raunana ƙarfin mayaƙan a yankin, yayin da waɗanda suka tsira suka gudu zuwa cikin ƙasar Cameroon bayan fafatawar.