Dubban Musulmai daga sassan duniya sun fara gudanar da aikin Hajjin shekarar 1447/2026 bayan fara kwararowa zuwa Mina a ranar Litinin 8 ga watan Zul-Hijjah, ranar da ake kira Tarwiyah.

Mahajjatan na barin masaukansu a birnin Makka cikin farin ciki da tawali’u, suna masu amsa kiran Hajji da kalmar “Labbaikallahumma Labbaik”, yayin da maza ke sanye da fararen tufafin harami, mata kuma cikin tufafin da suka dace da ibada.

Ana sa ran kusan Musulmai miliyan biyu ne za su gudanar da aikin Hajjin bana, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Saudiyya ta bayyana.

Ranar Tarwiyah ita ce farkon ayyukan Hajji, inda alhazai ke sanya harami da ƙulla niyyar Hajji kafin su nufi Mina domin gudanar da salloli da kwana a can kafin tafiya filin Arfa.

A kwanaki masu zuwa, alhazai za su gudanar da muhimman ibadu da suka haɗa da tsayuwar Arfa da kwana a Muzdalifa da jifan jamarori da yanka hadaya da dawafi da sa’ayi tsakanin Safa da Marwa.

Tsayuwar Arfa a ranar tara ga Zul-Hijjah ita ce mafi muhimmancin rukuni na aikin Hajji, inda alhazai za su taru suna addu’o’i da ibada kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar.

Gwamnatin Saudi Arabia ta ce ta kammala shirye-shirye domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin tsaro da walwala, inda ta tanadi dubban jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya da kuma tantunan Mina da aka gina da kayayyakin da ba sa kamawa da wuta.