Tsohon Sanata Kabiru Gaya ya rasa tikitin takarar Sanatan Kano ta Kudu na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) duk da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar ta amince da Kassim Batayya a matsayin ɗan takarar sasanci na mazabar Sanatan Kano ta Kudu a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da ke Miller Road.
Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan Gaya ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa NDC yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa a jihar Kano kafin zaɓen 2027.
An ruwaito cewa Gaya, wanda ya shafe shekaru a APC kafin ficewarsa, yana shirin komawa majalisar dattawa karkashin inuwar NDC.
Tsohon ɗan majalisar ya yi murabus daga APC a ranar 5 ga Afrilu, inda ya fara shiga ADC kafin daga bisani ya koma NDC tare da Rabiu Musa Kwankwaso.
Sai dai duk da hasashen cewa zai samu tikitin Kano ta Kudu, jam’iyyar ta zabi Kassim Batayya a lokacin zaɓen fidda gwani.
Mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, ne ya bayyana hakan ta wani saƙo da ya wallafa a Facebook ranar Lahadi.
Hassan ya kuma wallafa wani bidiyo inda Kabiru Gaya ya bayyana goyon bayansa ga Batayya a matsayin ɗan takarar sasanci na jam’iyyar.
A cikin bidiyon, Gaya ya ce duk da cewa ba ya wajen lokacin da aka yanke hukuncin, ya amince da sakamakon domin haɗin kan jam’iyyar.
Ya ce dukkaninsu suna aiki ne domin cigaban jam’iyyar, kuma siyasa tana buƙatar haƙuri da sadaukarwa.
A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne muradun jam’iyyar da kuma makomar Kano ta Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa NDC ta fara gudanar da zaɓukan fidda gwani ga masu neman takarar Sanata, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jiha domin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Masu lura da harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan ci gaban na iya sauya yanayin siyasar Kano ta Kudu, musamman yayin da ake sa ran ƙara tsanantar hamayya tsakanin manyan ɓangarorin siyasa a jihar.
Kabiru Gaya ya taba zama gwamnan jihar Kano tsakanin 1992 zuwa 1993 a jamhuriya ta uku, sannan daga bisani ya wakilci Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2023 karkashin APC.
A zaɓen 2023, ya sha kaye a hannun Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila wanda ya yi takara karkashin jam’iyyar NNPP.
Daga baya Sumaila ya koma APC, kuma rahotanni na nuna cewa ya samu tikitin jam’iyyar mai mulki domin sake neman kujerar Sanatan Kano ta Kudu a 2027.