Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun sace mutane 10 a fadar Sarkin Yashikira da ke ƙaramar hukumar Baruten a jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Adetoun Ejire-Adeyemi a ranar Litinin, ta ce maharan sun kuma kai hari ofishin ’yan sanda na Yashikira da misalin ƙarfe 2 na dare ranar Litinin.
Sanarwar ta ce Yan bindigar, cikin wani hari na haɗin gwiwa sun kai farmaki hedikwatar rundunar ’yan sanda ta Yashikira da kuma fadar Sarkin Yashikira.
A yayin harin maharan sun kuma banka wa wani ɓangare na fadar wuta, yayin da suka yi awun gaba mutane goma, inda jami’an ’yan sanda da ke bakin aiki suka yi nasarar daƙile harin da aka kai ofishin ’yan sandan.
Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba ko kuma ta tsorata da barazanar masu aikata laifuka da ke aiki a ko’ina cikin jihar, kuma za su yi duk mai yuwa wajen dawo da mutanen da aka sace