Alhaji Aminu Ado Bayero ya shirya gudanar da taron addu’a domin neman zaman lafiya da ci gaban Kano da Arewaci da ƙasa bakiɗaya.
Sanarwar na cikin takardar gayyata da sakataren Sarkin, Malam Abdullahi Haruna Kwaru ya sanya wa hannu.
Takardar ta ce za a gudanar da taron addu’ar ne a ranar Litinin 25 ga watan Mayu, 2026 da ƙarfe 10:00 na safe a fadar Sarkin da ke gidan Nassarawa.
Ya ce, za a yi addu’ar ne domin samun ingantaccen zaman lafiya da karuwar arziki a Kano da jihohin Arewa tare da roƙon Allah Ya ba da ikon yin zaɓen 2027 lafiya.