Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto aƙalla mutane 92 daga hannun mayaƙan Boko Haram, tare da kwance wasu nakiyoyi da ƴan ta’addan suka dasa a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya da ke ƙaramar hukumar Biu.


Sanarwar da kakakin rundunar musamman ta ‘Operation Haɗin Kai’ Laftanat Kanal Sani Uba ya fitar, ta ce mutanen da dakarun Najeriyar suka ceto sun haɗa da maza 52, da mata 33 da kuma ƙanan yara 7.


Dakarun Najeriyar, sun gano gungun ƴan ta’addan ne a lokacin da suke kora mutanen da suka sace tare da ababen hawansu zuwa cikin daji, bayan da suka gano ana biye da su ne kuma suka dasa nakiyoyi guda uku a kan hanya, da zummar daƙile yunƙurin ceton na sojin Najeriya, sai dai ba tare da ɓata lokaci ba, dakarun suka kwance baki ɗayan bama-baman.