Najeriya ta ci gaba da riƙe kambunta na ƙasa ta uku da tafi kowace kasa karɓan bashi daga Hukumar Bunƙasa Ƙasa da Ƙasa (IDA), reshen Bankin Duniya da ke bayar da rance mai sauƙin biya a duniya, duk da an biya wasu, akwai kudaden da suka rage mata a zangon farko na shekarar 2026.
A cewar bayanan kuɗi na IDA na watan Maris na Shekarar 2026, kudin da hukumar ke bin Najeriya ya kai dala biliyan 18.5 zuwa ranar 31 ga Maris, 2026, wanda ya ɗan ragu kadan daga dala biliyan 18.7 da aka samu a ƙarshen watan Disamba 2025.
Raguwar dala miliyan 200n na nufin an samu ragin kaso 1.1 cikin ɗari a cikin watanni uku. Sai dai idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, bashin Najeriya ya ƙaru sosai da dala biliyan 1.2, wato kaso 6.9 cikin ɗari, daga dala biliyan 17.3 da aka samu a watan Maris 2025.
Sabon jadawalin ya nuna cewa, Najeriya na biyewa Bangladesh da Pakistan a cikin ƙasashen da suka fi karɓar rancen kudi daga Bankin Duniya