Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan ci gaba da lalata layin dogo a wasu sassan ƙasar nan musamman a jihohin Filato da Bauchi.
Shugaban Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya, Dakta Kayode Opeifa ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a birnin Legas.
Sanarwar ta ce an samu sabbin hare-haren lalata layin dogo a jihohin Filato da Bauchi, lamarin da gwamnatin ta bayyana a matsayin barazana ga tsaro da ci gaban ƙasa.
Sanarwar ta ce irin waɗannan ayyuka na iya jawo hatsarin jirgin ƙasa, rasa rayuka da kuma lalata dukiyar gwamnati da aka kashe biliyoyin Naira wajen ginawa.