Wannan na cikin sanarwar da Amir Abdullahi Kima, mamba a Kwamitin Kar-takwa na Yaƙi da Fatauci da Safarar Miyagun Kwayoyi, Muggan Makamai da Ƙananan Yara da Gwamnatin Kano ta kafa ya fitar.


Sanarwar ta ce jami’an Civil Defence, NDLEA, ’yan sanda da Immigration ne suka haɗa hannu wajen gudanar da samamen ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin, Major A. A. Usman mai ritaya.


Yayin sumamen an gano jabun magungunan a cikin wani kango inda ake adana su cikin matsanancin zafi ba tare da kulawa mai kyau ba, sannan ba su da sahalewar Hukumar NAFDAC.