Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi.


Ya ce zaben shekarar 2027 ba zai kasance na kalamai ko siyasar ra’ayi kawai ba, illa yana bukatar shugabanci mai kwarewa da zai iya tunkarar matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar Najeriya.