An rantsar da Romuald Wadagni a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Benin a wannan Lahadi, bayan nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga watan Afrilu.
Tsohon ministan kuɗin ƙarƙashin gwamnatin Patrice Talon ya yi rantsuwar kama aiki ne a gaban Kotun Tsarin Mulki, tare da halartar wakilan ƙasashe sama da 15, ciki har da ƙaramar ministar Faransa mai kula da hulɗa da ƙasashen waje.
Abin da ya ja hankali a bikin shi ne halartar wakilai daga ƙasashen ƙungiyar AES — Burkina Faso da Mali da Niger — duk da rashin jituwar siyasa da aka dade ana samu tsakaninsu da gwamnatin Benin.
A jawabinsa na farko bayan rantsarwa, Wadagni wanda ke dab da cika shekaru 50, ya yi alƙawarin yin aiki domin bunƙasa Benin, kare mutuncin al’umma da kuma tabbatar da walwala da ƴancin jama’a kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
Game da matsalar tsaro da hare-haren masu iƙirarin jihadi a arewacin ƙasar, shugaban ya ce zai yi aiki tare da ƙasashen maƙwabta domin tunkarar barazanar.
Masana siyasa na ganin halartar Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, a bikin wata alama ce da ke nuna yiwuwar sassauta takun-saƙar da ke tsakanin Benin da Nijar tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a shekarar 2023.
Tun bayan takunkuman da ECOWAS ta kakaba bayan juyin mulkin ne aka rufe iyakokin Benin da Nijar, kuma har yanzu ba a buɗe su ba.
Shi kuwa tsohon shugaban Benin, Patrice Talon, zai koma zauren Majalisar Dattawa bayan sauka daga mulki, domin kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa duk wani tsohon shugaban ƙasa mai rai mamba ne kai-tsaye a majalisar.