Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce an cimma matsaya kan yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ƙasarsa da Iran.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da shugabannin wasu ƙasashen Larabawa da kuma Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.

Ya ce daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa akwai batun sake buɗe mashigar Hormuz, wacce ke da muhimmanci wajen jigilar mai a duniya.

Trump ya ƙara da cewa yanzu haka ana tattauna mataki na ƙarshe kafin a sanar da cikakken abin da aka cimma.

Sai dai kafar yaɗa labarai ta Fars, mai alaƙa da dakarun juyin juya halin Iran, ta ce mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon Iran.