Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a wani hari da aka kai wa jirgin ƙasa ɗauke da jami’an soji a birnin Quetta da ke kudu maso yammacin Pakistan, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Sai dai wasu majiyoyi na cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu ya fi haka, yayin da mutane da dama suka samu munanan raunuka.
Fashewar ta haddasa gobara a wasu daga cikin taragaggin jirgin, tare da lalata gidaje da motoci da ke kusa da wurin.
Jami’ai sun ce an dasa abin fashewar ne a cikin wata ƙaramar mota da aka ajiye kusa da layin dogo kafin ta tashi.
Rahotanni sun ce da dama daga cikin fasinjojin jirgin na kan hanyarsu ne domin halartar bukukuwan Babbar Sallah.
Ƙungiyar masu ɗauke da makamai ta Balochistan Liberation Army ta ɗauki alhakin kai harin.