Ma’aikatar Harkokin Waje ta Iran ta bayyana cewa Amurka, a matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashen da za su karɓi bakuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA, tana da alhakin bai wa tawagar ƙwallon ƙafar Iran bizar shiga ƙasar duk da saɓanin siyasa tsakanin ƙasashen biyu.


Kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin Iran na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa babu wata matsala da za ta hana tawagar ƙasar halartar gasar da za a gudanar a Amurka.

“’Yan wasanmu za su je Amurka ne kawai domin buga Gasar Kofin Duniya,” in ji Baghaei yayin wani taron manema labarai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Mehr ya rawaito.


Ya ƙara da cewa ƙasar mai masaukin baki tana da cikakken alhakin tabbatar da sauƙaƙa wa dukkan ƙasashen da suka cancanta shiga gasar, tare da jaddada cewa dole ne a bai wa tawagar Iran biza ba tare da la’akari da batutuwan siyasa ba.

Baghaei ya kuma bayyana fatan cewa hukumar FIFA za ta ɗauki matakan da suka dace domin kare martabarta da tabbatar da bin dokokin gasar.


Ya ce Iran za ta ci gaba da amfani da duk wata dama da take da ita domin tabbatar da halartar tawagarta cikin kwanciyar hankali da nasara.