Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu jimillar ƙuri’u 915,840 a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihohin Kano da Borno gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A Jihar Kano, Tinubu ya samu ƙuri’u 500,852 inda ya kayar da abokin takararsa guda ɗaya, Mista Osifo Osayamen Stanley, wanda ya samu ƙuri’u 2,675 a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
An sanar da sakamakon a hukumance ranar Asabar yayin tattara sakamakon da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.
A Jihar Borno kuwa, Gwamna Babagana Zulum ya ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na APC bayan ya samu ƙuri’u 414,988 a ƙananan hukumomi 27 na jihar.