Jam’iyyar PRP a Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓukan fidda gwani domin tantance ƴan takarar da za su tsaya mata takara a babban zaɓen 2027.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya shaida wa BBC cewa jam’iyyar ta bi dukkan sharuddan doka kafin fara zaɓukan fidda gwanin da za a gudanar a faɗin ƙasar ranar Litinin 25 ga watan Mayun 2026.

Ya ce PRP ta samu nasarar cimma matsaya a mafi yawan muƙamai, sai dai a takarar shugaban ƙasa inda aka samu rashin jituwa tsakanin masu neman takarar.

A cewarsa, mutum biyar ne suka nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar, amma daga baya aka rage su zuwa uku bayan tantancewa.

Ya bayyana cewa dukkan ƴan takarar shugaban ƙasar da aka amince da su sun fito ne daga kudancin Najeriya — daga jihohin Abia da Edo da kuma Cross River.

Dr Baba-Ahmed ya ce jam’iyyar za ta gudanar da zaɓukan fidda gwani ga kusan ƴantakara 300 a matakai daban-daban a faɗin Najeriya.

Ya ƙara da cewa a wuraren da mutum guda ne kawai ya nemi takara, jam’iyyar za ta tabbatar da shi kai tsaye ba tare da zaɓe ba.

Shugaban na PRP ya kuma ce babu wani ɗan arewacin Najeriya da ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar, abin da ya ce ya taimaka wajen karya raɗe-raɗin da ke cewa PRP jam’iyya ce ta Arewa kawai.

A halin yanzu dai jam’iyyu da dama a Najeriya sun fara gudanar da zaɓukan fidda gwani ko kuma amfani da tsarin maslaha domin rage rikice-rikicen cikin gida kafin zaɓen 2027.