Hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan wa’adin da Hukumar Zaɓe ta Najeriya, INEC, ta gindaya wa jam’iyyun siyasa ya haifar da sabon yanayi a siyasar ƙasar, musamman ga ƴan siyasar da ke son sauya sheƙa kafin zaɓen 2027.
Kotun ta ce INEC ba ta da ikon tilasta wa jam’iyyun siyasa lokacin da za su kammala zaɓukan fidda gwani ko gabatar da sunayen ƴantakara, inda ta mayar da wa’adin tattara bayanan mambobi zuwa watan Satumban 2026.
Mai shari’a M.G. Umar ya bayyana cewa dokar zaɓe ta bai wa INEC damar sanya ido kan zaɓukan cikin gida na jam’iyyu da kuma karɓar sunayen ƴantakara, amma ba ta ba ta ikon kakaba wa jam’iyyun wa’adin kammala tsare-tsarensu ba.
Masu sharhi kan siyasa na ganin cewa hukuncin zai ƙara buɗe ƙofa ga ƴansiyasar da suka rasa tikitin jam’iyyunsu ko kuma suke jin an yi musu rashin adalci, domin yanzu suna da ƙarin lokaci na sauya sheƙa zuwa wasu jam’iyyu kafin zaɓe.
Jam’iyyun adawa da dama sun yi maraba da hukuncin, suna masu cewa zai ba su damar karɓar sababbin mambobi da kuma sake tsara dabarunsu kafin zaɓen 2027.
Tun bayan hukuncin ne wasu ƴansiyasa suka fara sauya sheƙa, ciki har da ɗan majalisar dokokin Kano mai wakiltar Gwale, Hon. Abdulmajid Isa Umar Mai Rigar Fata, wanda ya fice daga APC zuwa jam’iyyar NDC bayan rashin samun tikitin takara.
Masana siyasa na hasashen cewa hukuncin zai iya ƙara yawan sauya sheƙa a watanni masu zuwa, yayin da ƴansiyasa ke neman sabbin damar takara kafin babban zaɓen 2027.