Aƙalla mutum 82 ne suka mutu, yayin da wasu biyu suka ɓace bayan fashewar gas a wani mahaƙar ma’adinan kwal a arewacin China, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.
Jami’an ceto sun sake rage adadin waɗanda suka mutu bayan sun fara sanar da cewa mutum 90 ne suka rasa rayukansu.
Fashewar ta afku ne a mahaƙar ma’adinan Liushenyu da ke lardin Shanxi, kuma ana kallonta a matsayin mafi muni da aka samu a China tun shekarar 2009.
Rahotanni sun ce ma’aikata 247 ne ke bakin aiki lokacin da lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7:29 na safiyar Juma’a agogon GMT.
An ceto fiye da mutum 100 daga cikin ma’aikatan, yayin da aka tura ɗaruruwan jami’an agaji domin ci gaba da aikin ceto.
Shugaban China, Xi Jinping, ya ce gwamnati za ta ci gaba da kula da waɗanda suka jikkata tare da ƙoƙarin gano waɗanda har yanzu ba a san inda suke ba.
Majalisar dokokin ƙasar ta ce za a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin, tare da hukunta duk wanda aka samu da sakaci.
Hukumomi sun kuma ba da haƙuri kan ruɗanin da aka samu game da adadin waɗanda suka mutu, inda suka ce mutum 128 na ci gaba da jinya a asibitoci, ciki har da biyu da ke cikin mawuyacin hali.