Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Amurka da Iran na dab da cimma yarjejeniya ta ƙarshe kan tattaunawar da ke gudana tsakanin ɓangarorin biyu.
Trump ya bayyana cewa zai amince ne kawai da yarjejeniyar da ta dace da muradun Amurka, kamar yadda ya shaida wa CBS.
Ya kuma jaddada cewa duk wata yarjejeniya za ta tabbata ne idan Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, tare da miƙa sinadarin uranium ɗinta.
A cewarsa, idan Iran ba ta amince da waɗannan sharuɗɗa ba, “ba zai yiwu a ci gaba da tattaunawa ba.”