Hukumomin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Kongo sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa birnin Bunia da ke yankin Ituri har zuwa wani lokaci, saboda fargabar yaɗuwar cutar Ebola.

A wata sanarwa da ma’aikatar sufuri ta ƙasar ta fitar, ta ce jiragen ɗaukar kayan agaji da na ma’aikatan lafiya ne kaɗai za a dinga tantancewa domin ba su izinin sauka, bayan amincewar hukumomin lafiya da na zirga-zirgar jiragen sama.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne domin hana yaɗuwar cutar tare da kare lafiyar fasinjoji da ma’aikatan jirage da kuma na filayen jiragen sama.

Gwamnatin ta kuma buƙaci kamfanonin jiragen sama da su bi duk matakan kariya da hukumomin lafiya suka gindaya.

Bunia na daga cikin yankunan da cutar Ebola ta fi kamari a halin yanzu.

Ba kasafai gwamnatin Kongo ke dakatar da zirga-zirgar jiragen sama sakamakon ɓarkewar Ebola ba, domin a lokuta da dama kamfanonin jiragen sama ne kan ɗauki irin wannan mataki da kansu.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sama da mutum 170 ne ake zargin sun mutu tun bayan ayyana sabon ɓarkewar cutar.

A gefe guda kuma, maƙwabciyar ƙasar Uganda ta sanar a ranar Asabar cewa an sake gano wasu mutum uku da suka kamu da cutar, lamarin da ya kai adadin masu ɗauke da ita zuwa biyar.