Sarkin Maroko Mohammed na shida ya yi afuwa ga wasu magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal da aka daure bayan samun su da hannu a tayar da tarzoma a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a birnin Rabat a watan Janairun 2026.

An saki magoya bayan ne a wani mataki na jin ƙai da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Maroko da Senegal, musamman yayin da ake shirin gudanar da Babbar Sallah.

Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya bayyana a shafinsa na X cewa nan ba da jimawa ba magoya bayan za su koma wajen iyalansu.

“Ina miƙa godiyata ga mai martaba saboda wannan mataki na tausayi da mutuntaka,” kamar yadda shugaban ya wallafa.

A watan da ya gabata ma an saki wasu magoya bayan Senegal uku bayan sun kammala zaman watanni uku a gidan yari.

An yanke wa magoya bayan Senegal 18 hukuncin ɗauri ne bayan sun kutsa cikin filin wasa a lokacin da aka bai wa Maroko bugun fenariti a wasan ƙarshe na gasar.