A makon da ya gabata, hankalin ’yan Najeriya ya sake komawa kan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, bayan wasu zarge-zarge masu tayar da hankali da Muhammad Musa Kamarawa, kusa a wajen Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, ya yi. Kamarawa ya yi zargin cewa wasu jami’an ’yan sanda biyu sun “kashe” ɗan gwagwarmayar a gabansa.

Wannan furuci ya sake tayar da hankalin mutane da dama a Najeriya waɗanda suka daɗe suna neman sanin inda Dadiyata yake. Yanzu shekaru bakwai kenan tun bayan da matashin ɗan gwagwarmayar ya ɓace bayan wasu mutane da ba a san ko su waye ba, waɗanda ake zargin jami’an tsaro ne, suka sace shi a ƙofar gidansa da ke unguwar Barnawa a Jihar Kaduna.

A yanzu haka, mutane da dama suna kira ga hukumomi da su gudanar da bincike kan kalaman Kamarawa domin gano gaskiyar abin da ya faru da Dadiyata.


Abin da Kamarawa Ya Faɗa

A wani saƙo da ya wallafa a Facebook ranar Laraba, Muhammad Musa Kamarawa — tsohon Mataimaki na Musamman ga Bello Matawalle a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara — ya yi zargin cewa wasu jami’an ’yan sanda biyu sun harbe Dadiyata a gabansa.

“Jami’an ’yan sandan da nake zargi, CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba, sun bincike ni, sun kwace kuɗina, sannan suka binciki gidana ba tare da sammacin kotu ba. Sun yi barazanar za su ‘kashe’ ni kamar yadda suka ‘kashe’ Dadiyata da wasu a gabana a Operation Yaki da ke Kaduna…,” in ji shi.

Domin ƙara tabbatar da zargin nasa, bayan wani mai amfani da Facebook ya tambaye shi cewa:

“Don Allah da sunan Allah, da gaske ne sun kashe Dadiyata a gabanka…?”

Sai Kamarawa ya amsa da rantsuwa:

“Wallahi tallahi, Hussaini Gimba ne ya kashe shi,” in ji Kamarawa.