A ranar Juma’a ne China ta sanar da faɗaɗa cire haraji kan kayayyakin da ake shigar mata daga dukkan ƙasashen Afirka da ke da alaƙar diflomasiyya da ita, a wani mataki da ke da nufin ƙarfafa kasuwanci da bunƙasa masana’antu a nahiyar, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito.
A ƙarƙashin sabon tsarin, ƙasashen Afirka 53 ne za su amfana da cire harajin shigo da kaya, ciki har da Nijeriya da Kenya da Masar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Sabuwar manufar ta ƙara faɗaɗa tsarin da China ta riga ta aiwatar, wanda ya bai wa ƙasashe 33 mafi ƙarancin ci gaba a Afirka damar shigar da kayayyaki ba tare da haraji ba.
A ranar Juma’a ɗin ne kuma aka karɓi jigilar kaya ta farko da ta amfana da sabon tsarin tan 24 na tuffa daga Afirka ta Kudu a birnin Shenzhen, lamarin da ke nuna fara aiwatar da shirin a hukumance.
Mahukuntan kasuwanci na China sun ce matakin zai taimaka wajen ƙarfafa fitar da kayayyakin Afirka zuwa kasuwannin China, musamman kayayyaki irin su cocoa da coffee da ‘ya’yan itatuwa da kuma inabi.
A baya, irin waɗannan kayayyaki kan fuskanci harajin da ya kai tsakanin kashi takwas zuwa talatin cikin ɗari kafin sabon tsarin ya fara aiki.