Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya zargi matatar mai ta Dangote da yunƙurin mamaye kasuwar man fetur ta ƙasar ta hanyar ƙalubalantar lasisin shigo da mai da aka bai wa wasu kamfanonin da ke gogayya da ita, kamar yadda takardun kotu da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani suka nuna.
A cikin bayanan kariya da ya gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, NNPC ya ce idan har aka amince da buƙatar Dangote na soke ko rage yawan lasisin shigo da mai, hakan na iya haddasa matsala wajen samar da mai, da rashin daidaiton farashi, tare da barazana ga tsaron makamashin Nijeriya.
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya, NMDPRA, ita ma ta nemi shiga cikin shari’ar, lamarin da ya ƙara faɗaɗa takaddamar kan manufofin shigo da mai da kuma tasirin matatar Dangote a kasuwar man fetur.
Matatar Dangote, wacce ta fara tace ɗanyen mai a shekarar 2024, ita ce mafi girma a Afirka, inda take da ƙarfin tace ganga 650,000 na mai a kowace rana.
Shari’ar na zuwa ne watanni kaɗan kafin matatar ta fara gudanar da cikakkun ayyukanta a watan Satumba, lamarin da ke haifar da tambayoyi kan yadda kasuwar mai za ta kasance, da irin tasirin da hakan zai yi ga masu zuba jari.
A watan Afrilu ne matatar Dangote ta shigar da ƙara tana ƙalubalantar lasisin shigo da mai da Hukumar NMDPRA ta bai wa wasu dillalan mai da kuma NNPC.
Dangote ya ce yawaitar ba da lasisin shigo da mai na hana bunƙasar tace mai a cikin gida, kuma hakan ya saɓa wa tanade-tanaden Dokar Masana’antar Man Fetur ta Nijeriya.