A cikin takardar ƙorafin mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Mayu, 2026, Farfesa Usman Yusuf ya ce kalaman sun biyo bayan sharhin da ya yi kan haɗakar siyasa da kuma batutuwan siyasar yankuna.

Ya bayyana cewa ko da yake Sanata Kwankwaso bai ambaci sunansa kai tsaye ba, amma bayanin da ya yi ya isa ya sa masu sauraro gane wanda ake nufi.

Farfesa Yusuf ya kuma yi zargin cewa Sanatan ya bukaci magoya bayan Kwankwasiyya da wasu ƙungiyoyin matasa su “tarwatsa” wanda ake magana a kansa da kalmar Hausa ta “fata-fata,” lamarin da ya ce na iya jawo tsoratarwa ko tashin hankali.