Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin kudin cin abinci mai lafiya ga mutum guda a Najeriya ya kai N1,513 a kowace rana a watan Fabrairu.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahotonta na “Cost of a Healthy Diet (CoHD)” na watan Fabrairu 2026 da aka fitar a Abuja.

A cewar NBS, wannan adadi ya karu da kashi 3.76 idan aka kwatanta da N1,458 da aka samu a watan Janairu 2026.

Hukumar ta bayyana cewa CoHD shi ne mafi arha hadin abinci daga cikin kayan abinci na gida da ake samu, wanda ke cika ka’idojin abinci mai gina jiki da aka amince da su a duniya.

Ta ce ana amfani da wannan ma’auni ne wajen auna damar jama’a ta samun abinci mai lafiya ta fuskar kudin shiga da samuwa.

A cewarta, wannan adadi baya hada kudin sufuri ko na shirya abinci, sai dai farashin abinci kawai.

Rahoton ya nuna cewa yankin Kudu maso Gabas ne ya fi tsada wajen cin abinci mai lafiya da N1,889 a kowace rana, sai Kudu maso Yamma da N1,786.

A gefe guda kuma, Arewa maso Gabas ce ta fi rahusa da N1,160 a kowace rana.

A matakin jihohi, Ekiti, Imo da Abia sun fi kowace jiha tsada wajen cin abinci mai lafiya, yayin da Adamawa, Borno da Taraba suka fi rahusa.

Hukumar ta ce farashin abinci mai lafiya ya ci gaba da tashi a cikin shekarar da ta gabata, inda ya karu da kashi 12.4 idan aka kwatanta da Fabrairu 2025.

Ta kuma bayyana cewa abincin dabbobi shi ne ya fi tsada a cikin rukunin abinci, duk da cewa yana samar da kaso 13% kacal na kuzarin da ake bukata a jiki.

Haka kuma, ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari suna daga cikin mafi tsada idan aka kwatanta da adadin kuzarin da suke bayarwa.

Rahoton ya kara da cewa legumes, kwayoyi da tsaba su ne mafi rahusa a cikin nau’ukan abinci.

NBS ta ce wadannan sakamakon na da matukar muhimmanci wajen taimaka wa gwamnati da masu tsara manufofi wajen inganta tsaron abinci da rage wahalar samun abinci mai lafiya a Najeriya.