Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa (ICPC) ta kare matakin da ta dauka na hana shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tana mai cewa matakin ya yi daidai da umarnin kotu da ke kan lamarin.
Kakakin hukumar, John Odey, ne ya bayyana haka ga PUNCH Online a ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani kan zargin da ADC ta yi na cewa an hana shugabanninta shiga kuma an nuna musu rashin mutunci yayin ziyarar da suka kai ranar Juma’a.
Odey ya ce ICPC ta riga ta mayar da martani ga wasikar da ADC ta aike tana neman izinin ziyartar El-Rufai, inda aka yi musu bayani cewa ba za a amince ba.
Ya ce jam’iyyar ta aike da sunayen wasu shugabanni da suka hada da Aregbesola da Abolaji Abdullahi da wasu.
A cewarsa, ICPC ta karɓi wasikar a ranar 20 ga wata sannan ta mayar da amsa a ranar 21 ga wata, inda ta umarci su da kada su zo saboda umarnin kotu a bayyane yake.
Ya bayyana cewa umarnin kotu ya takaita masu izinin ganin El-Rufai ne kawai ga iyalansa na kusa, lauyoyinsa da kuma likitocinsa.
A cewarsa, duk wanda ba ya cikin wadannan rukuni uku ba shi da damar shiga domin ganin tsohon gwamnan.
Odey ya kuma musanta zargin cewa jami’an tsaro sun yi wa shugabannin ADC barazana ko cin zarafi a hedikwatar ICPC da ke Abuja.
Ya ce kasancewar ‘yan sanda masu makamai a kofar hukumar abu ne na yau da kullum na tsaro, ba wai don tsoratar da kowa ba.
A cewarsa, ICPC ba siyasa take yi ba, kuma tana bin doka ne kawai wajen aiwatar da umarnin kotu da kuma tabbatar da tsaron wanda ake tuhuma.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin umarnin kotu da ya takaita masu damar ziyartar El-Rufai yayin da yake fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume tara da suka shafi zargin karya dokokin cin hanci da rashawa da kuma wasu dokokin jihar Kaduna.
El-Rufai dai ya musanta dukkan tuhumomin da ake masa a gaban kotu.