Fiye da mahajjata miliyan 1.5 daga kasashe daban-daban sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana, lamarin da ya zarce adadin bakin hajjin da suka halarci aikin hajji daga kasashen waje a shekarar 2025.

Wani jami’in Saudiyya ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce duk da rikice-rikicen da suka faru a yankin Gabas ta Tsakiya, mahajjata sun ci gaba da tururuwa zuwa kasar domin sauke farali.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a watan Fabrairu ya haddasa matsaloli a harkar zirga-zirgar jiragen sama bayan Tehran ta kai hare-hare kan wasu wurare a Saudiyya da yankin Gulf.

Wannan ya jawo dakatar da zirga-zirgar jirage a wasu lokuta tare da tashin farashin tafiye-tafiye.

Sai dai manyan kamfanonin jiragen sama a kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar da Bahrain sun yi kokarin dawo da ayyukansu yadda ya kamata bayan makonni na rufe sararin samaniya da soke wasu jirage.

Duk da wadannan kalubale, mahajjata sun ci gaba da zuwa Saudiyya domin halartar aikin Hajjin bana.

Kwamandan rundunar kula da fasfo na aikin Hajji ta Saudiyya, Saleh Al-Murabba, ya ce adadin mahajjatan da suka iso daga kasashen waje ya kai mutum 1,518,153 zuwa yanzu.

Ana sa ran adadin zai ci gaba da karuwa a cikin kwanaki biyu masu zuwa yayin da karin mahajjata ke ci gaba da shigowa kafin fara manyan ibadun Hajji a ranar Litinin.

A shekarar da ta gabata, jimillar mahajjatan da suka gudanar da aikin Hajji sun kai mutum 1,673,320, ciki har da mahajjata 1,506,576 daga wajen Saudiyya.

Aikin Hajji na daya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar, kuma wajibi ne ga duk Musulmin da Allah Ya ba hali su yi shi a kalla sau daya a rayuwarsu.