Babbar Kotun Tarayya ta Najeriya ta sanar da rasuwar daya daga cikin alkalanta masu zaman kansu, Mai shari’a Mohammed Yunusa na bangaren shari’a na Kano.

Daraktar yada labarai ta kotun, Catherine-Oby Christopher, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Asabar.

Sanarwar ta ce Mai shari’a Yunusa ya rasu ne ranar Alhamis bayan gajeriyar rashin lafiya a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano.

An kuma bayyana cewa an riga an yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

Kotun ta bayyana marigayin a matsayin fitaccen masani a harkar shari’a wanda ya yi aiki da kwarewa, gaskiya da cikakken sadaukarwa wajen tabbatar da adalci.

A cewar sanarwar, gudunmawar da Justice Mohammed Yunusa ya bayar ga bangaren shari’a da harkar lauya za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa.

Kotun ta kara da cewa abokan aikinsa, lauyoyi, ma’aikatan kotu da duk wadanda suka yi aiki tare da shi za su yi kewarsa sosai.

Babban Alkalin Kotun Tarayya, alkalan kotun, mahukunta da ma’aikata sun mika ta’aziyyarsu ga iyalansa tare da yi musu addu’ar Allah ya ba su hakurin jure wannan babban rashi.

Sanarwar ta kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.