Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kusan mutane miliyan 35 a Najeriya na cikin hadarin fama da matsananciyar yunwa daga watan Yuni zuwa Agusta na wannan shekara.
Kungiyar kula da harkokin jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hakan a birnin New York na kasar Amurka, inda ta ce Najeriya na fuskantar karin matsalar karancin abinci yayin da lokacin fari da wahalar samun abinci ke kara matsowa.
A cewar rahoton, kusan mutum daya cikin mutane bakwai a Najeriya na iya fuskantar matsananciyar rashin wadataccen abinci a watanni masu zuwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Najeriya yanzu na daga cikin kasashen duniya da ke fama da babbar matsalar yunwa, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Rahoton ya ce idan ba a gaggauta kai dauki ba, iyalai da dama za su tilasta rage yawan abincin da suke ci, sayar da kadarorinsu ko kuma cire ‘ya’yansu daga makaranta domin tsira.
Majalisar ta kuma bayyana cewa kimanin yara miliyan 6.4 a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Najeriya na cikin hadarin fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki a wannan shekara.
Saboda haka, Majalisar Dinkin Duniya tare da abokan hulɗarta sun yi kira da a samar da tallafin gaggawa domin fadada ayyukan ceton rayuka.
A cewar rahoton, shirin bayar da agajin jin kai na shekarar 2026 wanda aka ware dala miliyan 516 domin aiwatarwa, ya samu kasa da rabin kudaden da ake bukata.
Rahoton ya nuna cewa zuwa watan Mayun 2026, an samu kusan dala miliyan 215 ne kacal daga cikin dala miliyan 516 da ake bukata domin gudanar da ayyukan agajin jin kai a Najeriya.