Mutanen da ake zargi da kai harin sace dalibai da malamai a makarantu uku da ke garuruwan Esinele, Yamota da Alawusa a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo sun bude hanyar tattaunawa da gwamnatin jihar.

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa masu garkuwar sun ki yin magana da iyalan wadanda aka sace, inda suka ce suna son tattaunawa kai tsaye da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, kuma wannan ne sharadin da suka bayar.

Wata majiya ta ce har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin tattaunawar ko bukatun masu garkuwar ba domin kare rayukan wadanda ke hannunsu.

Har yanzu ba a tabbatar ko gwamnan ne da kansa ke jagorantar tattaunawar ko kuwa wakilan gwamnati ne ke gudanar da ita ba, amma wata majiya ta bayyana cewa bude hanyar sadarwa wani abin kwantar da hankali ne.

Majiyar ta kara da cewa jami’an tsaro sun san yadda za su gudanar da aiki, amma lamarin yana da hadari sosai saboda rayukan wadanda aka sace.

Lokacin da aka tuntubi mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Abayomi Fagbenro, ya ki cewa komai kan lamarin.

Fargaba kan lafiyar yara kanana

Rahotanni sun nuna cewa malamai da dalibai ciki har da yara kanana masu shekaru biyu zuwa uku na cikin wadanda aka sace. Yanzu haka sun shafe sama da mako guda a hannun masu garkuwar.

Iyaye da shugabannin al’umma sun nuna damuwa musamman saboda damina ta fara, wanda hakan ke sa zirga-zirga a dazuka da wurare masu wahala ya zama cikin hadari.

Majiyoyi daga yankunan da abin ya shafa sun ce masu garkuwar na yawo da wadanda suka sace a cikin dazuka da kuma tsakanin jihohi domin kauce wa jami’an tsaro.

Wani shugaban al’umma wanda ya nemi a boye sunansa ya ce har yanzu mazauna yankin ba su san inda wadanda aka sace suke ba, kuma suna cikin tsananin damuwa musamman ganin akwai kananan yara a cikinsu.

Makarantu sun fara zama babu dalibai

Lamarin ya jawo tsoro sosai a Ogbomoso da wasu yankuna makwabta kamar Ikose, Ikoyi, Tewure da Dananu, inda dalibai da dama suka daina zuwa makaranta.

Bincike ya nuna cewa yawan daliban da ke halartar makarantu na gwamnati da masu zaman kansu ya ragu sosai saboda tsoron rashin tsaro.

Malamai ma sun tabbatar da cewa iyaye, dalibai da ma’aikatan makarantu na cikin fargaba duk da kokarin gwamnati na kwantar da hankali.

Wata malama daga makarantar firamare ta Ikose ta ce tun bayan harin, makarantu da dama sun zama babu dalibai sosai. Ta kara da cewa tsoro ya karu bayan wasu dalibai a makarantar Areago Grammar School sun yi zargin sun ga ‘yan ta’adda a kusa da makarantar, wanda hakan ya jawo firgici.

A yayin rikice-rikicen da suka biyo baya, wani dalibi ya mutu bayan mota ta buge shi, sannan rahotanni suka ce mahaifiyarsa ma ta mutu bayan samun labarin rasuwarsa.

Malamar ta ce yawan dalibai da malamai ya ci gaba da raguwa yayin da mutane ke komawa gida tun kafin lokacin tashi saboda tsoro.

Wata malama daga Tewure ta ce iyaye da dama sun kira ta suna sanar da ita cewa ba za su bari ‘ya’yansu su ci gaba da zuwa makaranta ba saboda tsoron abin da ya faru a Esinele.

Malamai sun shiga cikin tashin hankali

Tsoron malamai ya karu bayan kashe wasu malamai biyu a harin.

Daya daga cikin wadanda aka kashe shi ne tsohon mataimakin shugaban makaranta, Joel Adesiyan, yayin da wani malami mai suna Michael Oyedokun aka ce an kashe shi bayan yana hannun masu garkuwa.

Malaman sun bayyana cewa lamarin ya jefa su cikin tashin hankali, inda wasu ke tunanin daina zuwa makarantu da ke yankunan karkara saboda tsaro.

Wata malama mai suna Oyeyemi ta ce wasu iyaye kan dauki ‘ya’yansu daga makaranta tun kafin a tashi saboda jita-jitar yiwuwar sake kai hari.

Ta ce abin da ake bukata yanzu shi ne karin jami’an tsaro a makarantu da yankunan karkara domin dawo da kwarin gwiwar jama’a.

Gwamnati ta dora laifi kan labaran karya

Kwamishinan yada labarai na jihar Oyo, Dotun Oyelade, ya ce wasu labaran karya da bidiyoyi da ake yadawa a kafafen sada zumunta ne suka kara tsananta tsoro a tsakanin jama’a.

Ya zargi wasu masu wallafa labarai da yada bidiyoyi marasa inganci domin tada hankalin mutane.

A cewarsa, gwamnatin jihar na ci gaba da kokarin kwantar da hankalin jama’a tare da tabbatar musu cewa ana aiki domin dawo da tsaro.

An yi jana’izar malamin da aka kashe cikin alhini

A ranar Juma’a, an yi jana’izar Joel Adesiyan mai shekaru 49 a Ogbomoso cikin alhini da jimami.

Jami’an gwamnati, shugabannin kungiyar malamai ta NUT, ‘yan uwa da sauran jama’a sun halarci jana’izar inda suka bukaci a tabbatar da adalci tare da kubutar da sauran wadanda aka sace.

A sakon da aka karanta a madadin gwamna Seyi Makinde, gwamnatin jihar ta bayyana alhini kan lamarin tare da tabbatar da cewa ana kokarin ganin an kubutar da wadanda ke hannun masu garkuwa lafiya.

Iyalan malamin da aka kashe sun bayyana jimaminsu

Iyalan Michael Oyedokun, malamin da aka ce an kashe a hannun masu garkuwa, sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi mai raɗaɗi.

Mai magana da yawun iyalan ya ce marigayin ya shafe sama da shekaru 20 yana koyarwa a makarantun gwamnati kuma mutum ne mai saukin kai da son zaman lafiya.

Iyalan sun kuma bayyana cewa marigayin bai bar ko da yaro guda ba duk da cewa ya yi aure fiye da shekaru 10.

Sun roki ‘yan Najeriya da su daina yada bidiyoyi da hotunan da ke nuna yadda aka kashe shi saboda hakan na kara jefa iyalan cikin damuwa da tashin hankali.

Lamarin ya sake tayar da muhawara a Najeriya kan matsalar rashin tsaro da kuma hadarin da malamai da dalibai ke fuskanta musamman a yankunan karkara.