Mataimakin gwamnan jihar Lagos, Obafemi Hamzat, ya lashe zaɓen fidda gwani na APC domin takarar gwamna a 2027 bayan samun ƙuri’u 657,917 cikin 657,974 da aka kaɗa. Abokin takararsa Lanre Jim-Kamal ya samu ƙuri’a ɗaya kacal.
Shugaban kwamitin zaɓen, Janar Jon Temlong mai ritaya, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana a sakatariyar APC da ke Ikeja.
Hamzat ya gode wa Shugaba Tinubu, Gwamna Sanwo-Olu da shugabannin APC bisa goyon baya, sannan ya gabatar da tsarinsa na “My Lagos Dream” wanda ya mayar da hankali kan ayyukan yi, ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da tsaro.