Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fara biyan albashin watan Mayu ga dukkan ma'aikatan gwamnati kafin bikin Eid al-Kabir domin ba su damar yin shirye-shiryen Sallah cikin sauki.

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Yada Labarai da Al'adu ta jihar ta fitar, Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu, Alhaji Mahmud Muhammad Dantawasa, ya ce matakin ya nuna kudirin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na kula da walwalar ma'aikata da iyalansu.

Gwamnatin ta bayyana cewa biyan albashin da wuri zai taimaka wajen rage wa ma'aikata matsin tattalin arziki da ke tattare da lokutan bukukuwa, musamman a wannan lokaci da iyalai da dama ke fuskantar kalubalen rayuwa.

Gwamnatin ta yaba wa ma'aikatan jihar bisa jajircewa da

biyayya wajen gudanar da ayyukansu, tare da kira ga al'ummar Zamfara da su yi amfani da lokacin Babbar Sallah wajen karfafa zaman lafiya, hadin kai da yi wa jihar da Nijeriya addu'ar ci gaba da tsaro.