Shugabannin jam’iyyar ADC na kasa sun koka kan yadda jami’an hukumar ICPC suka hana su ganin Nasir El Rufai, yayin wa ziyar da suka kai inda ake tsare da shi.
Tawagar ADC wadda ta kunshi sakataren jam’iyyar Rauf Aregbesola da Sakataren yada labaran jam’iyyar Bolaji Abdullahi da kuma Salihu Lukman, sun ziyarci El Rufai domin tattaunawa kan wasu batutuwa, amma basu samu damar ganin El Rufai ba.
A martanin da ta fitar, hukumar ICPC ta ce kotu bata bawa ‘yan siyasa da abokan El Rufai damar ganinsa a inda yake tsare ba.