Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce gwamnatinsa za ta rage farashin man dizel a ƙasar domin tallafa wa masu amfani da shi, biyo bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya.


A cikin makon nan, masu motocin sufurin haya a Kenya sun gudanar da yajin aikin kwanaki biyu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu kusan 30. Wannan mataki ya faru ne saboda fushin jama’a kan tsadar man fetur da ta janyo tsadar rayuwa.


A cikin jawabin nasa a talabijin, Ruto ya ce ya bayar da umarnin rage farashin dizel a tsarin farashi na watannin Yuni zuwa Yuli domin taimakawa wajen daidaita farashin a gidajen mai da kuma kawo ƙarin sauƙi ga talakawa.


A makon da ya gabata ne Kenya ta ƙara farashin sayar da mai da kusan kashi 23.5% na tsarin farashi na watannin Mayu da Yuni, a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarancin ɗanyen mai a duniya da kuma tsadar makamashi sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya.