Masarautar Zazzau ta dakatar da shugaban ƙauyen Matarawa bisa zargin damfara da cin zarafin al’umma a harkokin rabon gado.


A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar, Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya gargaɗi hakimai da shugabannin ƙauyuka da su guji cutar da jama’a musamman a harkokin rabon gado.


Sanarwar ta ce Sarkin ya umarci hakimai da su sanya ido sosai kan yadda shugabannin ƙauyuka ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum da al’umma.


Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa bayan kammala dawo da kuɗaɗen da aka karɓa, Sarkin ya karɓi kuɗin sannan ya miƙa su ga Hakiman Kudan da Hunkuyi da ke ƙarƙashin masarautar.