Shugaban ALGON na Jihar Kaduna Muhammad Jamilu Abubakar Albani ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce babu gaskiya a rahoton da Sahara Reporters ta wallafa cewa shugabannin kananan hukumomi na karbar kasa da naira miliyan 25 duk wata duk da tarin kudaden da ake turo musu daga gwamnatin tarayya.
Ya ce gwamnatin Kaduna ta samar da tsarin biyan albashi ta hanyar fasahar zamani na e-payment tare da tabbatar da biyan albashi, fansho da sauran hakkokin ma’aikata kai tsaye bisa hukuncin kotun koli na cin gashin kan kananan hukumomi.
Kungiyar ta kuma bukaci Sahara Reporters da su fito da hujjoji ko sunayen shugabannin kananan hukumomin da ake dangantawa da zargin, tare da neman kafar ta janye rahoton tare da bayar da hakuri cikin sa’o’i 48.