Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da:

Engr. Marwan Ahmad – Kwamishinan Ayyuka

Dr. Abubakar Labaran Yusuf – Kwamishinan Lafiya

Dr. Dahir Muhammad Hashim – Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi

Dr. Danjuma Mahmoud – Kwamishinan Noma da Albarkatun Kasa

Dr. Gwani Ali Haruna Abubakar Makoda – Kwamishinan Ilimi

Hon. Abduljabbar Umar Garko – Kwamishinan Kasa da Tsare-tsaren

Hon. Abdulkadir Abdussalam – Kwamishinan Raya Karkara da Al’umma

Hon. Adda’u Lawan Kutama – Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman, Ofishin Majalisar Zartarwa

Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa – Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a

Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo – Darakta Janar

Hajiya Nana Asma’u Jibrin – Darakta Janar na fannin Bincike da Adana Bayanai

Alhaji Umar Jalo, wanda zai kasance sakataren kwamitin.

An ɗora wa kwamitin alhakin shirya gagarumin bikin tunawa da cika shekara uku na gwamnatin tare da nuna nasarori da ayyukan da gwamnatin ta samu.

Ana sa ran Gwamna Yusuf zai kaddamar da kwamitin da karfe 3:00 na yammacin ranar Juma’a, 22 ga Mayu, 2026 a dakin taro na Ofishin Majalisar Za