Gwamnatin Jihar Jigawa ta samar da kwale-kwalen gudu guda 20 domin ƙarfafa ayyukan kwashe mutane da bayar da agajin gaggawa a yankunan da ambaliya ke yawan shafa a jihar.
Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara na musamman kan muhalli, Hamza Muhammad, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Dutse.
Ya ce matakin zai tabbatar da saurin kwashe mutanen da ambaliya ta rutsa da su a al’ummomin da ke fama da ambaliya.