Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar demokkuradiyyar Congo,Samuel Kamba ya bayyana cewa cutar da ta bullu a ƙasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 153,daga cikin mutane 626 da aka gano sun kamu da ita.
Ministan ya bayyana yankunan Ituri dake karkashin ikon jihar Bunia da yankin Mongwalu ida lamarin ya fi kamari,duk da cewa akwai wasu yankuna da cutar ta bullu.
Ya zuwa wannan lokaci,arewacin Kivu ne cutar ta bayyana inda aka gano mutum daya da ya kamu da ita a Goma,biyu a Butembo,wacce ba ta tsaya a nan ba,ta kuma bazu zuwa kudancin Kivu.
Rahotanni daga yankunan da ke karkashin ikon ƴan tawayen M23, an samu bulluwar cutar bayan gano mutun daya da ya kamu da cutar a garin Mitiu.
A Rwampara, kimanin kilomita goma daga Bunia, dangin wani majiyyaci da ya mutu sakamakon cutar Ebola sun cinawa tantunan cibiyar kula da marasa lafiya wuta a jiya Alhamis.