Ministan Tsaro Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci na daga cikin manyan barazanar da ke addabar ƙasar nan.
Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da wani littafi mai taken ayyukan yaki da Ta’addanci da tada Ƙayar Baya a Arewa maso Gabas, Wanda tsohon Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta MNJTF kuma tsohon Shugaban Kwalejin horas da sojoji Manjo Janar Ibrahim Yusuf mai ritaya ya rubuta.
Christoper Musa ya jaddada cewa nasarar kawar da ta’addanci na buƙatar haɗin kai da jajircewar rundunar soji, hukumomin gwamnati da kuma al’umma baki ɗaya.
Ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro domin ganin an samu nasara a fatattakar yan ta’addan, yana mai cewa rundunar soji kaɗai ba za ta iya magance ƙalubalen tsaron da ake fuskanta ba.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya buƙaci dakarun tsaro su ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas tare da ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa.