Mai bawa Gwamnan Jihar Oyo shawara ta musamman kan harkokin tsaro Abayomi Fagbenro ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta dake cewa an sako mutanen da aka sace a harin da aka kai makarantu uku a Karamar Hukumar Oriire a ranar Juma’ar da ta gabata ba gaskiya ba ne.
Harin da aka kai makarantun ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum biyu tare da sace kusan malamai da ɗalibai 30.
Tun daga daren ranar Laraba, rahotannin ke cewa an sako malamai da ɗaliban da aka sace a harin.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai game da tabbatar da sahihancin labarin, mai bawa gwamanan shawara kan harkokin tsaron ya ce har zuwa jiya Alhamis ba a sako malamai da ɗaliban da yan ta’addan suka yi garkuwa da su ba.